Bani da masaniyar cewa gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa muka je fashi ba – Barawo

Bani da masaniyar cewa gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa muka je fashi ba – Barawo

Rikakken dan fashi da makami Mohammed Yusuf wanda ya jagoranci gungun barayin da suka kai farmaki gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya bayyana cewa a cikin rashin sani suka afka gidan Sanatan.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Yusuf mai shekaru 25 ya bayyana haka ne a yayin da yansanda suka yi bajakolinsa ga manema labaru a babban ofishin Yansandan Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja.

bKU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya sake nada mataimakiyarsa wani babban mukami a gwamnatin Kaduna

Sai dai Yusuf ya kara da cewa basu tarar da jami’in Dansanda ko daya ba a gidan Sanatan a yayin da suka shiga gidan da nufin yi masa fashi da makami, inda yace ta katangar gidan suka haura suka fada gidan, sa’annan suka yi amfani da karfen Jack wajen bude kofar guda daga cikin dakunan gidan.

Bani da masaniyar cewa gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa muka je fashi ba – Barawo

Ike da Barawo
Source: Twitter

Bugu da kari shugaban yan fashin ya bayyana cewa sun shiga gidan ne da nufin neman kudi, amma sai suka kare basu samu komai ba, sai ma kama shi da aka yi yayin da sauran abokan satarnasa suka ranta ana kare.

“Wanda muka fara gani da muka shiga gidan shine dan Ekweremadu, inda muka tursasa masa ya yi mana jagora har zuwa dakin babansa, a lokacin ne ya fara kiran sunan babannasa, nan da nan mahaifin ya bude kofar dakinsa

“Amma da fari mun dauka yaron yana kiran sunan matarsa ne domin kuwa ‘Honey Honey’ yake cewa, kwatsam sai muka ga katon namiji ya fito daga cikin daki” Inji shi.

Da yake jawabi a yayi bajakolin barawon, kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Jimoh Moshood ya bayyana cewa a iya binciken da suka gudanar, basu fahimci wata manufa ta bindige mataimakin shugaban majaisar ba, don haka yace zargin da ake yi na wasu na kokarin halaka Sanatan ba gaskiya bane.

Daga karshe ya tabbatar ma manema labaru cewa matsala ce ta kananan barayi kawai ba wani abu ba, sa’annan ya kara da cewa rundunar Ynsandan za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron lafiyar Sanatan da ta sauran yan Najeriya gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel