Buhari ya nuna alhini kan mutuwar Sarkin Nasarawa

Buhari ya nuna alhini kan mutuwar Sarkin Nasarawa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhini bayan ya samu labarin mutuwar sarkin Nasarawa, Alhaji Hassan Ahmed Abubakar II.

A wata sanarwa daga mai ba shi shawara a kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina a Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Nuwamba, shugaban kasar ya mika ta’aziyya ga iyalai da masarautar Nasarawa.

Ya kuma yi ta’aziyya ga gwamnati da mutanen jihar Nasarawa kan mutuwar babban basaraken.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa baza’a taba mantawa tare da karramar sarkin ba waen ganin ya kawo zaman lafiya, sasanci da kuma ci gaban Najeriya.

Buhari ya nuna alhini kan mutuwar Sarkin Nasarawa

Buhari ya nuna alhini kan mutuwar Sarkin Nasarawa
Source: Depositphotos

Ya bukaci abokai da makusantan sarki da ci gaba da kare martabar sat a hanyar ci gaba da wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta sha kan yan Boko Haram a Yobe, sun dawo da kwanciyar hankali

Shugaban kasar ya kuma yi addu’a kan Allah ya ji kan ruhin Abubakar sannan ya ba mutanensa juriya da kuma madadinsa na alkhairi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel