Kurunkus: Gwamnatin tarayya ta gano babban kalubale ga zaman lafiyar Najeriya

Kurunkus: Gwamnatin tarayya ta gano babban kalubale ga zaman lafiyar Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce yawaitar matasan da ba su da aikin yi na matukar barazana ga tsaro da cigaban Najeriya.

Babban sakatare a ma'aikatar matasa da wasanni, Mista Olusade Adesola, ne ya sanar da hakan yayin wani taro da ma su ruwa da tsaki a kan bullo da hanyoyin samawa matasa aikin yi da aka yi a Abuja.

Kungiyar kwadago ta kasa da kasa da hadin gwuiwar ma'aikatar wasanni da matasa ne su ka dauki nauyin taron.

Kurunkus: Gwamnatin tarayya ta gano babban kalubale ga zaman lafiyar Najeriya

Kurunkus: Gwamnatin tarayya ta gano babban kalubale ga zaman lafiyar Najeriya
Source: Depositphotos

A jawabinsa yayin taron, Adesola ya bayyana cewar babu wani abu da ke barazana ga harkar tsaro da zaman lafiya a Najeriya kamar matsalar rashin aiki a tsakanin matasa.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Atiku ya yi karin albashi ga duk masu aiki karkashinsa

Adesola ya kara da cewar akwai bukatar a gaggauta daukan mataki a kan matsalar rashin aikin yi a Najeriya saboda dalilan tsaro.

A nasa bangaren, Darektan kungiyar kwadago ta kasa da kasa a Najeriya, Mista Dennis Zulu, ya ce shirin su na kawo cigaba a kasashe ya fi mayar da hankali ne wajen samar da aiki ga matasa.

Kazalika, ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Ngige, ya yabawa kungiyar ILO bisa hadin kan da take bawa Najeriya wajen warware kalubalen rashin aiki a Najeriya.

Ya kara da cewar gwamnatin shugaba Buhari ta damu matuka da matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa tare da bayyana cewar gwamnatin za ta cigaba da daukan matakan kawo karshen matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel