Ba da son ran mu ba: Wadanda suka fallasa katobarar ministan Buhari ta abincin Zakzaky sun yi magana

Ba da son ran mu ba: Wadanda suka fallasa katobarar ministan Buhari ta abincin Zakzaky sun yi magana

Gidan Talabijin na kan yanar gizo na Oak ya ba ministan Shugaba Buhari na watsa labarai, Alhaji Lai Mohammed hakuri game da sakin faifan bidiyon sa inda yake cewa gwamnatin tarayyar Najeriya tana kashe akalla Naira miliyan 3.5 duk wata wajen ciyar da shugaban 'yan shi'a Ibrahim El-Zakzaky.

Ministan labarai da al’adun Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kashe akalla miliyan uku da rabi a wata wajen ciyar da tsararren shugaban kungiyar mabiya akidar Shi’a a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky.

Ba da son ran mu ba: Wadanda suka fallasa katobarar ministan Buhari ta abincin Zakzaky sun yi magana

Ba da son ran mu ba: Wadanda suka fallasa katobarar ministan Buhari ta abincin Zakzaky sun yi magana
Source: UGC

Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa Aso Rock bayan taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya Laraba, 7 ga watan Nuwamba, 2018.

“Gwamnatin tarayya na kashe N3.5million kowani wata domin ciyar da shi ( Zakzaky)" Lai ya laburta ga manema labarai.

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel