Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya

Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya

- Gwamna Ifeanyi Okowa ya bukaci 'yan Najeriya su mayar da al'amurransu ga Allah saboda shi kadai ne zai iya warware matsalolinsu

- Okowa ya lura cewa akwai matsaloli masu yawa da ke adabar Najeriya amma ya zama dole 'yan Najeriya su dogara ga Allah

- Gwamna Okowa ya ce Allah ne kadai zai iya kawo karshe kashe-kashen da makiyaya ke yi a wasu sassan kasar

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa babu wani da zai iya magance manyan matslololin da ke adabar Najeriya ila Allah hakan ya sa ya bukaci mabiya addinin kirista da su cigaba da addu'a domin Allah ya kawo sauki a kasar.

DUBA WANNAN: Kuma dai: Wata hukumar gwamnati tarayya ta yi barazanar shiga yajin aiki

Legit.ng Hausa ta gano cewar Gwamna Okowa ya yi wannan kirar ne bukin ranar kungiyar kirista na Najeriya (CAN) na shekarar 2018 wanda akayi a jihar a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba.

Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya

Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya
Source: Facebook

Legit.ng Hausa ta gano cewar Gwamna Okowa ya yi wannan kirar ne bukin ranar kungiyar kirista na Najeriya (CAN) na shekarar 2018 wanda akayi a jihar a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba.

"Wannan lokaci ne da mutane za su koma ga Allah, Ya kamata kowane kirista a Najeriya ya yiwa kasar addu'a domin Allah ya zartas da abinda ya yi niyya ga kasar; dole sai mun jure, mun cigaba da yin addu'o'i a ko yaushe; akwai kallubalai sosai amma dole mu koma ga Allah, Allah ne zai iya kawo karshen kashe-kashen da makiyaya ke yi.

"Muna bukatar gwamnatin tarayya ta zage damtse kan magance matsalar kashe-kashen makiyaya, domin muddin gwamntin bata zage damtse ba, hukumomin tsaro ba za su iya tabuka abinda ya fi yadda su keyi yanzu ba.

"Ya kamata muyi imani da Allah a matsayinmu na kirista, idan muka dage da yin addu'a zai amsa addu'o'in mu ya kawo karshen matsalolin da ke damun mu a kasar nan," inji Gwamna Okowa kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel