Zaben 2019: Amurka ta yi na'am da shirin hukumar INEC

Zaben 2019: Amurka ta yi na'am da shirin hukumar INEC

Kasar Amurka ta ce tana kyautata zaton cewa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta na Kasa INEC za ta gudanar da sahihiyar zabe a shekarar 2019 idan akayi la'akari da nasarar da hukumar ta samu a 2015 da kuma irin shirye-shiryen da hukumar keyi karkashin jagorancin Farfesa Mahmoud Yakubu.

Mataimakin sakataren harkokin Afirka, Ambassada Tibor Nagy ya bayyana cewa aikin da ke gaban hukumar abu ne mai wahala amma idan kowa ya bawa hukumar hadin kai za a samu nasara.

Tibor ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin shugaban INEC, Farfesa Yakubu a gidan jakadancin Amurka da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Zaben 2019: Amurka ta yi imani da hukumar INEC

Zaben 2019: Amurka ta yi imani da hukumar INEC
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Ya ce: "Najeriya ta zama abin kwantance ga sauran kasashen da ke nahiyar Afirka idan ana batun yadda ake tafiyar da harkokin mulkin demokradiyya."

Da ya ke amsa tambaya kan yadda Amurka ke kallon zaben na 2019, Nagy ya sake jadada cewa Amurka ba ta da wani dan takara da take goyon bayan, ya kara d cewa: "Abinda muka damu dashi shine yadda aka gudanar da zaben ba wanda ya yi nasara ba."

Ya ce 'yan Najeriya suna da ikon su zabi duk wanda suke so domin yi musu jagoranci sai dai ya kamata zabe ya kasance babu magudi ko kuma daniyya ko makamanci haka.

Ya kuma shawarci 'yan siyasa da hukumomin tsaro su guji aikata duk wani abu da ka iya janyo tashin hankali da kawo cikas ga sakamakon zaben na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel