Ga ban tausayi, ga ban haushi: An damke barauniyar kifi a kasuwa

Ga ban tausayi, ga ban haushi: An damke barauniyar kifi a kasuwa

Yayinda muke ganin yadda rayuwa tayiwa mutane kunci a Najeriya, labarin wata mata da aka kama tana satan kifi ya yi matukar baiwa mutane tausayi da takaici.

Wani faifan bidiyo ya bayyana a shafukan ra’ayi da sada zumunta wanda ke nuna wata mata tana neman afuwa bayan an kamata tana satan kifi a jihar Legas.

A bidiyon, kana iya ganinta rike da katon kifi tana rokon mai kifin kuma mutane na tsaye suna kallonsu.

Yayinda halin yan Najeriya shine suburbudan duk wanda aka da laifin sata or konashi koi ta da wuta, jama’ar dake wajen suka cika muhawara kan cewa shin yunwa ya tuntsurata ko kwadayi.

Wasu sun ji tausayinta kuma sun alakanta abinda tayi da halin da Najeriya ke ciki.

Kalli bidiyon:

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel