Ba mu kara yadda: Musulmai a Filato sun bukaci a basu mukamin mataimakin gwamna 2019

Ba mu kara yadda: Musulmai a Filato sun bukaci a basu mukamin mataimakin gwamna 2019

Biyo bayan yadda aka yi ta cece kuce a kafofin yada labarai a cikin farkon satin nan game da zabin mace kuma musulma da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai yayi a matsayin mataimakiya a zaben da za'a yi a shekarar 2019, suma musulmai a jihar Filato sunyi magana.

Yayin da mutane da dama ke ganin tamkar gwamnan bai kyauta ba musamman ma ganin yadda jihar ke fama da tashe-tashen hankula da ke da alaka da addini da kanilanci, wasu kuma sun kafa hujja ne da jahohi irin su Filato inda sukace ba'a baiwa musulmai mukamin mataimaki duk kuwa da yawan su.

Ba mu kara yadda: Musulmai a Filato sun bukaci a basu nukamin mataimakin gwamna 2019

Ba mu kara yadda: Musulmai a Filato sun bukaci a basu nukamin mataimakin gwamna 2019
Source: Twitter

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan ne ma ya sa al'ummar musulmai daga jihar ta Filato kamar wani Lauya mai suna Lawal Ishaq ya bayyana cewa suma a ko don yawan su a jihar da yace yakai kusan kaso 40 cikin dari, ya kamata a basu mukamin mataimaki a zaben 2019 mai zuwa.

Babban lauyan ya kara da cewa kananan hukumomi kamar Wase da Jos ta Yamma musulmai ne suka fi yawa, haka nan kuma a kananan hukumomin Mngu, Quan’pan, Shendam, Bassa, Barkin Ladi da Jos ta Kudu duk akwai musulmai da yawan gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel