Rundunar soji ta sha kan yan Boko Haram a Yobe, sun dawo da kwanciyar hankali

Rundunar soji ta sha kan yan Boko Haram a Yobe, sun dawo da kwanciyar hankali

- Sojoji sun yi nasarar daidaita halin da Katarko a karamar hukumar Gujba da ke Yobe ciki bayan sun dakile yunkurin yan ta’addan na kai hari

- Kakakin rundunar, Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana cewa a take rundunar suka shiga aiki bayan sun samu bayani

- Sun kua kora yan ta’addan baya ta hanyar bude masu wuta

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa sun yi nasarar daidaita halin da Katarko a karamar hukumar Gujba da ke Yobe ciki bayan sun dakile yunkurin yan ta’addan na kai hari sansani sojoji a garin.

Kakakin rundunar, Birgediya Janar Texas Chukwu a wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 8 gwatan Nuwamba ya bayyana cewa a take rundunar suka shiga aiki bayan sun samu bayani sannan suka kora yan ta’addan baya ta hanyar bude masu wuta.

Rundunar soji ta sha kan yan Boko Haram a Yobe, sun dawo da kwanciyar hankali

Rundunar soji ta sha kan yan Boko Haram a Yobe, sun dawo da kwanciyar hankali
Source: Depositphotos

Sannan ya kuma ce wasu yan ta’addan sun tsere dajin da ke kusa amma ana ci gaba da kokari don ganin an kama su, sannan kuma cewa a yanzu haka soji na aikin kakkaba a yankin.

KU KARANTA KUMA: Mafi karancin albashi: Kaso 95 bisa 100 na gwamnonin kasar nan ba za su iya biya ba – Gwamna Umahi

Chukwu ya bukaci mazauna Yobe baki daya musaan Katarko da su ci gaba da harkokin gabansu sannan su kai rahoton duk wani abu da basu aminta da shi ba ko wani shige da fice a yankinsu ga hukumomin tsaro domin daukar mataki akan lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel