Zargin rashawa: PDP ta bukaci NIA, DSS, INTERPOL su gano Oshiomhole a duk inda ya buya

Zargin rashawa: PDP ta bukaci NIA, DSS, INTERPOL su gano Oshiomhole a duk inda ya buya

- Jam'iyyar PDP ta bukaci hukumar NIA, da INTERPOL da su taimaka wajen gano Adams Oshiomhole, wanda ya tsere awanni bayan da hukumar DSS ta fara tuhumarsa

- Jam'iyyar ta ce tserewar da Oshiomhole yayi, a wannan gabar da tuhumar ta dau zafi, alama ce da ke nuna cewa zargin da ake masa gaskiya ne

- Don haka, jam'iyyar PDP na bukatar APC da fadar shugaban kasa, da su gaggauta fito da Oshiomhole don fuskantar hukunci a kotu

Jam'iyyar PDP ta bukaci hukumar jami'an tsaro ta kwarareu NIA, da kuma takwararta na INTERPOL da su taimaka wajen gano Kwamred Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa, wanda ya tsere awanni bayan da hukumar DSS ta fara tuhumarsa kan zargin cin hanci da rashawa.

Jam'iyyar ta ce gaggauta barin kasar da Oshiomhole yayi, a wannan gabar da tuhumar ta dau zafi, abun zargi ne da kuma alamar da ke nuna cewa zargin da ake masa gaskiya ne, da kuma haska yadda fadar shugaban kasa ke bashi kariya.

A cikin wata sanarwa daga kakakin jam'iyyar, Kola Ologbinduyan, wacce aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis, jam'iyyar ta kalubalanci jam'iyya mai mulki ta APC na cewar wai bata san da cewar DSS na tuhumar Oshiomhole ba, duk da ta ce hatta shi kansa gwamnan Edo ba zai tsallake hukunci ba.

KARANTA WANNAN: Ruwan da aka tafka a daminar bana ya yi mummunar barna a matatar man Dangote

Zargin rashawa: PDP ta bukaci NIA, DSS, INTERPOL su gano Oshiomhole a duk inda ya buya

Zargin rashawa: PDP ta bukaci NIA, DSS, INTERPOL su gano Oshiomhole a duk inda ya buya
Source: Depositphotos

Sanarwar ta ce, yan Nigeria na sane da cewa Adam Oshiomhole bai yi ja-in-ja kan wannan zargi da akr masa ba, kuma bai boye gaskiyar magana na cewar APC da fadar shugaban kasa na sane da bahallatsar ba.

"Tuni dai dama PDP ta ke yiwa Oshiomhole gargadi kan taurin kunnensa, da kuma tsabar burin son shugabanci, ga kuma almubazzaranci da dukiyar jama'a, wanda mun tabbata zai kwashi kashinsa a gaban shari'a.

"Don haka, jam'iyyar PDP na bukatar APC da fadar shugaban kasa, da su gaggauta fito da Oshiomhole don fuskantar hukunci a kotu" a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel