Zamu tsige duk wani gwamna da ya ki biyan sabon albashi - Wabba

Zamu tsige duk wani gwamna da ya ki biyan sabon albashi - Wabba

Shugaban kungiyar kwadago na kasa (NLC), Ayuba Wabba ya bayyana cewa duk gwamnan da ya gaza biyan sabon albashi mafi karanci kamar yadda akayi yarjejeniya zai rasa kuri'un ma'aikatan jiharsa a zabe mai zuwa.

Ya yi kira ga ma'aikat suyi amfani da kuri'unsu da adadinsu wajen tsige duk wani gwamna da ya ki biyan sabon albashi saboda a cewarsa ba masu kaunar al'umma ba ne.

Wabba ya kallubalanci gwamnonin jihohi su fadawa ma'aikatansu abinda za su iya biya kana su ga sakayyar da ma'aikatan za suyi musu.

Zamu tsige duk gwamnan da ya ki biyan sabon albashi - Wabba

Zamu tsige duk gwamnan da ya ki biyan sabon albashi - Wabba
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Ya bayyana cewar yawancin gwamnonin suna boyewa karkashin inuwar kungiyar gwamnonin Najeriya domin gujewa bayyanawa ma'aikatansu abinda za su iya biya.

A wani rahoto mai alaka da wannan, Legit.ng Hausa ta kawo muku cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya yiwa dukkan ma'aikatan da ke karkashinsa karin albashi zuwa N33,000.

Mohammed El-Yakub, Direktan Gotel Communications, kamfanin sadarwa mallakar Atiku da ke Yola ya tabbatarwa Sahara Reporters a yau Alhamis inda ya ce, "za a fara biyan sabuwar albashin mafi karanci na N33,000 daga watan Nuwamban 2018 kuma karin albashin ya shafi dukkan wadanda ke aiki karkashin Atiku har da masu hidima a gidajensa."

El-Yakub ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kimanin mutane 100,000 da ke karbar albashi a kowanne wata a karkashin tsohon mataimakin shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel