'Yan bindiga sun sace dan takarar sanata da shugaban jam'iyyar ADC na jihar Ondo

'Yan bindiga sun sace dan takarar sanata da shugaban jam'iyyar ADC na jihar Ondo

- 'Yan bingida sunyi awon gaba da dan takarar Sanata da Ciyaman din jam'iyyar ADC a jihar Ondo

- 'Yan bindigan sun sace su ne a hanyarsu ta Akoko zuwa Akure babban birnan jihar Ondo

- Har yanzu 'yan bindigan ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace din ba domin neman kudin fansa

Yan bindiga sun sace mutane biyar ciki har da dan takarar sanata na mazabar Ondo ta Arewa a karkashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Jide Ipinsagba da ciyaman din jam'iyyar ta jihar Ondo, Bisi Ogungbemi.

'Yan bindiga sun sace dan takarar sanata na ADC da ciyaman din jam'iyyar

'Yan bindiga sun sace dan takarar sanata na ADC da ciyaman din jam'iyyar
Source: UGC

An sace su ne a hanyar Owo/Oba Akoko a hanyarsu ta Akoko zuwa Akure, babban birnin jihar ta Ondo.

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

'Yan bindigan da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace su ne misalin karfe 7 na yamma sannan su kayi awon gaba da su zuwa wani wuri da har yanzu ba a gano ba.

Sauran mutanen da ke tare da dan takarar sanatan da shugaban jam'iyyar da aka sace sun hada da direbansa, hadiminsa da kuma wani jigo a jam'iiyar da ADC, Prince Abdulkareem.

A lokacin rubuta wannan rahoton babu wani da ya tuntubi iyalan wadanda aka sace din domin neman kudin fansa kafin a sako su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel