Yanzu Yanzu: Mambobin majalisar wakilai sun koka kan rasa tikitin dawowa majalisa

Yanzu Yanzu: Mambobin majalisar wakilai sun koka kan rasa tikitin dawowa majalisa

Yan majalisar wakilai sun nuna bakin ciki da dacin rai a zaman majalisa na ranar Alhamis, 8 ga watan Nuwamba kan rashin mallakar tikitin dawowa majalisa wanda mafi akasarin yan majalisar ba su samu ba daga jam’iyyun siyasarsu.

Mambobin majalisar All Progressives Congress (APC) ne kan gaba wajen zargin shugaban jam’iyyar da kulla masu munakisa.

Gwamnonin jam’iyyar ma basu tsira ba a hannun yan majalisar da suka sanya masu suna a matsayin wadanda suka yi cuwa-cuwa lokacin zaben fidda gwani don kawai su tursasa zabinsu.

Yanzu Yanzu: Mambobin majalisar wakilai sun koka kan rasa tikitin dawowa majalisa

Yanzu Yanzu: Mambobin majalisar wakilai sun koka kan rasa tikitin dawowa majalisa
Source: Depositphotos

Musamman suka yi zargin cewa damokradiyyar jam’iyyar na tangal-tangal.

KU KARANTA KUMA: 2019: Allah ne kadai zai iya hana ni yin tazarce – Gwamna Emmanuel

Yan majalisar sun kuma bayyana cewa damokradiyar Najeriya na iya fuskantar barazana idan har majalisar dokokin kasar ta ci gaba da daukar raini daga wadanda ke ci gaba da karya dokar kundin tsarin mulkin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel