Majalisar wakilai ta bukaci Buhari ya gaggauta korar Maihaja daga shugabancin hukumar NEMA, sun bayyana dalili

Majalisar wakilai ta bukaci Buhari ya gaggauta korar Maihaja daga shugabancin hukumar NEMA, sun bayyana dalili

Majalisar wakilai ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kori shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Mustapha Maihaja, daga aiki saboda da samun sa da laifin almundahanar kudi fiye da biliyan N33bn da kwamitin majalisar ya yi.

A yau ne kwamitin da majalisar ta kafa ya mika rahoton da ke tabbatar da samun Maihaja da badakalar kudi tare da bayar da shawarar korar sa daga aiki.

Hukumar NEMA ba ta taba tsallake binciken zargin badakalar yadda ta ke tafiyar da al'amuranta ba, musamman yadda ta ke kashe kudaden da ta karba da kuma yadda ta ke sayen kaya domin rabawa ga ma su bukatar taimako.

Majalisar wakilai ta bukaci Buhari ya gaggauta korar Maihaja daga shugabancin hukumar NEMA, sun bayyana dalili

Majalisar wakilai
Source: Depositphotos

Ko a shekarar 2016, sai da kwamitin majalisar ya bankado yadda wasu jami'an hukumar ke sace kayan abinci da aka saya domin rabawa mazauna sansanin 'yan gudun hijira na jihar Borno.

A wani labarin mai alaka da majalisa da Legit.ng ta kawo ma ku, kun ji cewar shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, sanar da canje-canje a shugabancin wasu keamitoci a majalisar dattijai.

Biyo bayan canje-canjen, Sanata Lawal Gumau (dan jam'iyyar APC daga jihar Bauchi) ta zama sabon shugaban kwamitin kula da daidaito a rabon aiyukan gwamnatin tarayya.

DUBA WANNAN: Gwamnoni 6 da su ka bayyana a fili cewar za su iya biyan N30,000 ma fi karanci albashi

Gumau ya canji tsohon shugaban kwamitin, Sanata Tijjani Kaura (dan jam'iyyar APC daga jihar Zamfara), wanda yanzu aka bawa rikon kwamitin harkokin da su ka shafi hukumar 'yan sanda.

Kaura ya canji Sanata Abu Ibrahim (dan APC daga jihar Katsina), wanda yanzu aka bawa rikon kwamitin kula da bangarenk kwadago da daukan aiki.

Tsohon shugaban ma su rinjaye a majalisar ta dattijai, Sanata Ali Ndume (dan jam'iyyar APC daga jihar Borno), yanzu ya zama sabon shugaban kwamitin kula da hukumar ma'aikatan gwamnatin tarayya da a baya Sanata Paul Walker (dan PDP daga jihar Bayelsa) ke shugabanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel