Rikicin APC: Buhari da Amosun sun kara kebewa a Aso Rock

Rikicin APC: Buhari da Amosun sun kara kebewa a Aso Rock

An sake shiga wata ganawar sirri tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamna Amosun na daya daga cikin gwamnonin APC da zaben fidda 'yan takara da uwar jam'iyya ta yi bai yiwa dadi ba.

Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ya ki yarda ya mika sunan dan takarar gwamna Amosun a matsayin wanda dan takarar gwamna a jihar Ogun ga hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC).

Amosun na aga cikin gwamnonin APC da ke kokarin ganin sun kawar da Adams Oshiomhole daga shugabancin jam'iyyar APC.

Ragowar gwamnonin da ke son ganin an raba raba Oshiomhole da kujerar sa sun hada da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, da takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Rikicin APC: Buhari da Amosun sun kara kebewa a Aso Rock

Buhari da Amosun
Source: Facebook

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, rigingimun jam'iyyar APC na kara yin tsamari a tsakanin wasu jiga-jigan 'ya'yanta da shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole.

Ko a jiya, sai da jaridar Legit ta kawo ma ku rahoton cewar ministan sadarwa, Adebayo Shitu, da rufe ofishin yakin neman zaben shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo da ke Ibadan.

Ministan ya yi haka ne bayan burinsa na samun tikitin takarar gwamnan jihar Oyo a inuwar jam'iyyar APC bai cika ba.

DUBA WANNAN: Gwamnonin da su ka bayyana a fili cewar za su iya biyan ma fi karanci albashi

Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ne ya yi watsi da takarar ministan bayan samun sa da laifin kin yin bautar kasa lokacin da ya kammala karatun jami'a.

A satin da ya gabata ne aka ga wata babbar motar daukan kaya, a ginin MBO da Ofishin kamfen din Buhari/Osinbajo, na debe dukkan wasu kaya mallakar ministar zuwa wurin da babu ya sani.

Ma su aiki a ofishin yakin neman zaben sun ki cewa komai lokacin da manema labarai su ka tunkare su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel