2019: Allah ne kadai zai iya hana ni yin tazarce – Gwamna Emmanuel

2019: Allah ne kadai zai iya hana ni yin tazarce – Gwamna Emmanuel

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya ce Allah ne kadai zai iya hana shi yin tazarce a 2019.

Gwamnan wanda ya yi Magana a wani taro na yan jihar Akwa Ibom da ke Abuja da kuma jihohi 19 na arewa, yayi amfani da damar wajen nuna nasarorinsa tun bayan da hau mulki shekaru uku da suka gabata.

Ya ce shi ya yi imani da cewa mulki na Allah ne, bayan wasu mutane sun yi hasashen cewa jihar zai fuskanci yaki a lokacin zaben 2019.

2019: Allah ne kadai zai iya hana ni yin tazarce – Gwamna Emmanuel

2019: Allah ne kadai zai iya hana ni yin tazarce – Gwamna Emmanuel
Source: Depositphotos

Yace ziyarar da ya kaiwa yan asalin jihar a jihohin arewa 19 shine karo na farko da wani gwanmna mai ci zai yi hakan harma ya bude taron zantawa da mutanensa a Abuja.

Ya ce ya rigada ya roki Allah da ya yi amfani da shi wajen inganta jihar sannan kuma cewa babu inda mutane za su shiga a jihar ba tare da sun ga alamun ci gaba na gwamnatinsa ba.

KU KARANTA KUMA: Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta yi martani yayinda gwanatin tarayya ta karyata batun amincewa da N30,000

Udom ya yi alkawarin cewa idan har ya zarce toh kaso 80 na abincin da mutane za su dunga ci zai fito daga jihar ne.

Ya kuma lissafa asibitoci, makarantu, hanyoyin jihar daga cikin nasarorinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel