Da zafi zafi: Buhari ya kaddamar da dokar ta baci akan tsafta da samar da ruwa a Nigeria

Da zafi zafi: Buhari ya kaddamar da dokar ta baci akan tsafta da samar da ruwa a Nigeria

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da dokar ta baci kan tsafta, samar da ruwa a Nigeria, da kuma gyaran muhalli

- Buhari ya ce kaddamar da dokar ta bacin ya zama wajibi ne don rage yawaitar cututtukan da ake kamuwa dasu daga ruwa maras tsafta da kuma kazantar muhalli a fadin kasar

- Ya bukaci gwamnatocin jihohi da su yi koyi da wannan mataki don cimma muradun karni na shirin WASH kafin nan da shekarar 2030

A ranar Alhamis dinnan, rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da dokar ta baci kan tsafta, samar da ruwa a Nigeria, da kuma gyaran muhalli.

A cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara na musamman kan kafofin sadarwa da watsa labarai, Mr. Femi Adesina, shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta bacin ne a lokacin bukin kaddamar da wani sabon daftari na sake dawowa da shirin tsafta da samar da ruwa na kasa WASH a fadar shugaban kasa, Abuja.

Buhari ya ce kaddamar da dokar ta bacin ya zama wajibi ne don rage yawaitar cututtukan da ake kamuwa dasu daga ruwa maras tsafta da kuma kazantar muhalli a fadin kasar, a cewar sa, cututtukan da ake samu daga hakan, ya haifar da mutuwar mutane da dama.

KARANTA WANNAN: Ni ban shan giya - Dan sandan da aka kora bayan hasko shi rike da kwalbar giya

Da zafi zafi: Buhari ya kaddamar da dokar ta baci akan tsafta da samar da ruwa a Nigeria

Da zafi zafi: Buhari ya kaddamar da dokar ta baci akan tsafta da samar da ruwa a Nigeria
Source: Depositphotos

Buhari ya shaidawa mahalarta taron cewa yana sane da cewa Nigeria bata cimma bukatar hukumar dorewar muradun karni MDG kan tsafta da samar da ruwa ba, wanda shirin ya kare a 2015.

Ya ce: "Hukumar dorewar muradun kargin, na da bukatar cimma (6.1 da 6.2) na shirin WASH, inda a lokacin har ta bukaci tallafi daga WASH don samar da adadin yawan tsaftataccen ruwa a wuraren da ake bukatar hakan cikin farashi mai sauki.

"A wannan dalilin ne ma ya sa na yanke shawarar a yau, in tariyo zaman da mukayi da majalisar zartaswa ta kasa a watan Afrelu, don kaddamar da dokar ta baci kan fannin tsafta da samar da ruwa na kasar.

"Ina kira ga dukkanin gwamnatocin jihohi da su yi koyi da wannan mataki da na dauka kamar dai yadda al'adar hakan ta tanadar don bamu damar yin aiki kafada-da-kafada don cimma muradun karni na shirin WASH kafin nan da shekarar 2030," cewar shugaban kasa Buhari.

Ya kuma bayyana yawaitar yin ba-haya a bainar jama'a da kuma lalata bututun raba ruwa, a matsayin al'amuran da ke kawo cikas wajen ci gaban kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel