Kuma dai: Wata hukumar gwamnati tarayya ta yi barazanar shiga yajin aiki

Kuma dai: Wata hukumar gwamnati tarayya ta yi barazanar shiga yajin aiki

- Akwai yiwuwar hukumar sufurin jiragen sama na Najeriya za ta tsinduma cikin yajin aiki saboda rashin biyan wasu alawus din ma'aikatun ta

- Hukumar ta koka kan yadda gwamnatin tarayya ke jan jiki na tsawon shekaru bakwai ana yarjejeniya amma ba a cikawa

- Ma'aikatan hukumar sun bayyana cewa rashin biyan alawus din da cika sauran alkawurran na janyo cikas ga ma'aikata da abokan huldansu

Kishin-kishin: Hukumar sufirin jiragen sama kasa na shirin fara yajin aiki

Kishin-kishin: Hukumar sufirin jiragen sama kasa na shirin fara yajin aiki
Source: Twitter

A yayin da gwamnati ke kokarin warware matsalar yajin aiki na kungiyar kwadago da ASUU, akwai alamun cewar cikin 'yan makonni masu zuwa kungiyoyin da ke karkashin hukumar sufurin jiragen sama na Najeriya za su shiga yajin aiki saboda rashin biyan wasu alawus dinsu da gwamnati ba tayi ba.

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Hukumomin da za su shiga yajin aikin sune Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na Najeriya (FAAN), Kwallejin Koyar da Tukin Jiragen Sama (NCAT), Nigeria Civil Aviation Authority (NCAA), Cibiyar Kula da Sararin Samaniya (NAMA) da Nigeria Meteorological Agency (NiMet).

Wani da ke kusa da hukumomin ya shaidawa Sahara Reporters a yau Alhamis cewa babu wata dalili da zai sanya gwamnati ta rika jan jiki na tsawon shekaru bakwai bata cika alkawurran da ta dauka wa hukumomin ba.

Majiyar ta kara da cewa rashin cika alkawurran ya janyo tabarbarewar ayyuka da hukumomin kana yana karya lagwan ma'aikatan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel