Ni ban shan giya - Dan sandan da aka kora bayan hasko shi rike da kwalbar giya

Ni ban shan giya - Dan sandan da aka kora bayan hasko shi rike da kwalbar giya

- Hukumar rundunar 'yan sanda ta kori dan sandan da a baya bayan nan rahotonni suka karade kafafen watsa labarai akansa, wanda aka hasko shi rike da kwalbar giya

- Sai dai, dan sandan Kadima Useni, ya ce sam baya tu'ammali da wasu kayan maye da suka shafi giya, ya kwace kwalbar giyar ne daga hannun yaran wani jami'in dan sanda

- Mai magana da yawun rundunar, ya ce kwamishinan 'yan sanda ya gargadi jami'ai daga karbar wani abun sha na maye a lokacin da suke bakin aiki

Dan sandan da a baya bayan nan rahotonni suka karade kafafen watsa labarai akansa, wanda aka hasko shi rike da kwalbar giya, a layin Akowonjo, Dopemu da ke jihar Lagos, a jiya Laraba ne hukumar rundunar 'yan sanda ta kore shi daga bakin aiki.

Sai dai, dan sandan mai sheakru 42 da haihuwa, Kadima Useni, mai lambar aiki 176219, ya ce sam baya tu'ammali da wasu kayan maye da suka shafi giya, shi dai kawai ya kwace kwalbar giyar ne daga hannun yaran wani jami'in dan sanda.

Wani fai-fayen bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, ya nuna Useni, wanda ke aiki da rundunar ta 22 da ke Ikeja, rike da kwalbar giya.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N159m don gina wata babbar cibiya a asibitin AKTH

Ni ban shan giya - Dan sandan da aka kora bayan hasko shi rike da kwalbar giya

Ni ban shan giya - Dan sandan da aka kora bayan hasko shi rike da kwalbar giya
Source: Depositphotos

Wata majiya daga rundunar 'yan sanda, ta ce: "Sifeta Janar, Ibrahim Idris ne ya umurci kwamishinan 'yan sanda na jihar, Imohimi Edgal, da ya gurfanar da dan sandan don yi masa kyakkyawan hukuncin laifin da ya aikata."

Majiyar wacce ta ce a lokacin da aka cafko dan sandan, ya fara musanya shan giyar inda Useni ke cewa, "Ni ko kadan bana shan giya, na karbi kwalbar ne daga yaran wani jami'in dan sanda, wadanda ke wasa da ita. Daga baya, na kuma mayar masu da ita. Ban taba tunanin wai ana daukata bidiyo a lokacin ina rike da kwalbar giyar ba."

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ta jihar Legas, CSP Chike Oti, ya ce an cafke dan sandan ne tare da tuhumarsa, inda ya tabbatar da cewa shi ne wanda ke cikin bidiyon.

Mai magana da yawun rundunar, ya ce: "A wannan gabar, kwamishinan 'yan sanda ya gargadi jami'ai daga karbar wani abun sha na maye a lokacin da suke bakin aiki, duk wanda aka kama yana shan giya a bakin aiki kuwa to zai fuskanci hukunci kamar na Useini."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel