'Kashi 95 bisa dari na jihohi ba zasu iya biyan albashin N30,000 dinnan ba'

'Kashi 95 bisa dari na jihohi ba zasu iya biyan albashin N30,000 dinnan ba'

- Kaso 95 na jihohin kasar nan bazasu iya biyan N30,000 a mafi karancin albashi ba

- Jihohi da dama suna fama da gwamnati akan rashin biyan albashi

- Idan gwamnatin tarayya zata karawa jihohi kudaden shiga to za'a iya biya musu wannan bukata

'Kashi 95 bisa dari na jihohi ba zasu iya biyan albashin N30,000 dinnan ba'

'Kashi 95 bisa dari na jihohi ba zasu iya biyan albashin N30,000 dinnan ba'
Source: Facebook

A ranar Labara ne gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya bayyana ra'ayin sa akan karin albashi da ma'aikata suke nema ayi musu .

Gwamnan yace kashi 95 na jihohin dake fadin kasar na bazasu iya biyan mafi karancin albashin ma'aikata N30,000 ba.

Jihohin zasu iya biyan wadannan kudade ne idan har gwamnatin tarayya zata kara musu kudin shiga.

Jihohi da dama suna cikin matsala sannan basa iya biyan ma'aikata albashi sannan mutane suna zargin gwamnoni dakin yi musu aiki.

DUBA WANNAN: Yadda WHO ke ceton Najeriya

Mutane bazasu taba gane wannan matsalar ba saboda gwamnonin sunja bakin su sunyi shiru.

Yayi kira ga manyan kasa da kuma ma'aikata da suyi duba na tsanaki akan asusun gwamnati kafin su yanke hukunci.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel