Jihohi ne ya kamata sun yanke hukunci kan karancin albashi ba Gwamnatin Tarayya ba – El-Rufai

Jihohi ne ya kamata sun yanke hukunci kan karancin albashi ba Gwamnatin Tarayya ba – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa jihohi ne ya kamata su shirya albashi mafi karanci dai-dai da samun su,, ba wai gwanatin tarayya ba.

Ya bayyana hakan a jiya Laraba, 7 ga watan Nuwamba a Abuja lokacin taron kudaden shiga na kasa wanda kungiyar gwamnonin Najeriya ta shirya.

Ya ce idan aka duba kundin tsarin 1963 albashi afi karanci baya cikin lissafi na musaan. Cewa daga baya ne akan kara shi lokacin mulkin soja.

Jihohi ne ya kamata sun yanke hukunci kan karancin albashi ba Gwamnatin Tarayya ba – El-Rufai

Jihohi ne ya kamata sun yanke hukunci kan karancin albashi ba Gwamnatin Tarayya ba – El-Rufai
Source: UGC

Ya ce akwai dokoki da dama da lokacin soji ne aka zartar da su sannan kuma cewa akwai bukatar sake duba su sannan ayi wani abu a kai.

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki yace kudaden shiga ba zai habbaka ba idan babu ci gaba a tattalin arziki inda ya kara da cewa akwai bukatar tshe duk wata kafa ai yoyo.

KU KARANTA KUMA: A rufe duk wasu gidajen giya da ke kusa da harabar yan sandan Lagas – Edgal Imohimi ya yi umurni

A nashi bangaren gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya ce yayinda kasar ke shirin sanya dokar sabon albashi mafi karanci wanda zai kara nauyi kan kudaden jiha, akwai bukatar gwamnobi da dukkan masu fada a ji su yi duk abunda ya kamata domin daidaita tsakanin tattalin arziki da kudaden da ake kashewa ta hanyar kara kudaden shiga irinsu haraji, tara da sauransu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel