Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta yi martani yayinda gwanatin tarayya ta karyata batun amincewa da N30,000

Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta yi martani yayinda gwanatin tarayya ta karyata batun amincewa da N30,000

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba ta bayyana cewa N30,000 na karancin albashi da ke kunshe rahoton kwamitin da Gwanatin ta kafa shawara ne har yanzu ba wai sun amince da shi bane.

Ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed wanda ya yi Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron ako na majalisar zartarwa, yace sai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake nazari akan rahoton da aka gabatar asa a ranar Talata, kafin ya zartar da hukunci.

Amal Pepple yayinda take gabatar da rahoton a ranar Talata, ta bayyana cewa kwamitin sun bayar da shawarar cewa a kara albashi mafi karanci daga N18,000 zuwa N30,000 duk wata.

Ta kuma ce kwamitin ta rubuta wata doka cewa Gwanatin Tarayya zata tura shi ga majalisar dokokin kasar domin a chanja shi.

Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta yi artani yayinda gwanatin tarayya ta karyata batun amincewa da N30,000
Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta yi artani yayinda gwanatin tarayya ta karyata batun amincewa da N30,000
Asali: Depositphotos

Don haka kungiyar kwadago ta ce tana nan akan bakarta na N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

A halin yanzu, kungiyar kwadago ta yi barazanar cewa za su tafi yajin aiki idan har gwanati ta gaza amincewa da N30,000 da kwaitin ta bayar da shawara.

Babban sakataren kungiyar, Mista Musa Lawal ya bayyana hakan yayinda yake martani ga furucin inistan labarai, Lai Mohammed cewa shawara ce kawai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam’iyyar ADC da wasu 4

Lawal yace kungiyar kwadagon ta yanke shawarar ajiye yajin aikin da tayi niyar tafiya saboda gwamnati ta nuna shirin aincewa da rahoton.

Ya yi gargadin cewa da zaran ta ki yin abunda ya kamata toh za su tafi yajin aikin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel