Muna kashe miliyan N3.5m wajen ciyar da Zakzaky kowani wata – Gwamnatin tarayya (Bidiyo)

Muna kashe miliyan N3.5m wajen ciyar da Zakzaky kowani wata – Gwamnatin tarayya (Bidiyo)

Ministan labarai da al’adun Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kashe akalla miliyan uku da rabi a wata wajen ciyar da tsararren shugaban kungiyar mabiya akidar Shi’a a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky.

Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa Aso Rock bayan taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya Laraba, 7 ga watan Nuwamba, 2018.

“Gwamnatin tarayya na kashe N3.5million kowani wata domin ciyar da shi ( Zakzaky)" Lai ya laburta ga manema labarai.

Kalli bidiyon:

Mun kawo muku rahoton cewa ukumar Yan sanda na jihar Kaduna ta takaita zirga-zirga a wasu sassan jihar saboda cigaba da shari'ar shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria, Ibrahim El-Zakyzaky da za ayi a yau.

Yan sandan sun sake tunatar da al'ummar jihar cewar dokar hana zanga-zanga da tattaki da aka kafa a jihar har yanzu tana aiki saboda haka tana shawartar mazauna jihar suyi takatsantsan da inda za su tafi a yau.

Daga karshe, kotu ta hanashi beli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel