Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam’iyyar ADC da wasu 4

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam’iyyar ADC da wasu 4

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban jam’iyyar of African Democratic Congress (ADC) a jihar Ondo, Mista Bisi Ogungbemi a jihar. Sakataren labarai a jam’iyyar a jihar, Mista Idowu Akinrinlola ya tabbatar da lamarin a wayar tarho a ranar Alhais, 8 ga watan Nuwamba, Channels TV ta ruwaito.

A cewarsa, an yi garkuwa da Mista Ogungbei da wasu a yammacin ranar Laraba, 7 ga watan Nuwaba a hanyar Oba-Akko/Owo, yayinda suke hanyar tafiya daga Ikare –Akoko zuwa Akure, babbar birnin jihar.

Wadanda aka sace tare da shi sun hada da babban adiminsa, direbansa, da wani Jide Ipinsagba sai kuma wani jigon ADC a jihar, Princess Abdulkareem.

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam’iyyar ADC da wasu 4

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam’iyyar ADC da wasu 4
Source: UGC

Akinrinlola ya bayyana cewa an gano motocin wadanda aka sace a kan hanya yayinda aka kasa gano inda suke har yanzu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa wasu manyan APC su ka shigar da Adams Oshiomhole Kotu

Rundunar yan sandan jihar ma sun yi martani kan lamarin.

Kakakin yan sandan jihar, ista Fei Joseph yace an tura jami’an yan sanda zuwa wajen amma kawai otocinsu suka gano a kan hanya.

Ya kuma bayyana cewa zuwa yanzu yan sandan basu gano inda suke ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel