Fiye da lauyoyi 100 sun bayyana niyyarsu ta kare mutane 19 da suka kashe janar Alkali

Fiye da lauyoyi 100 sun bayyana niyyarsu ta kare mutane 19 da suka kashe janar Alkali

Akalla lauyoui dari da ashirin (120) ne suka bayyana aniyarsu ta fafatawa da rundunar Sojan kasa a gaban kotu domin su kare mutane goma sha tara (19) da hukumar Soji ke zargin suna da hannu cikin kisan gillar da aka yi ma wani hafsan Soja, Manjo janar Mohammed Alkali.

Majiyar Legit.com ta ruwaito lauyan mutanen 19, Gyang Zi ne ya bayyana haka a yayin daya nemi kotu ta bada belin wadanda ake zargi a gaban Alkalin babbar kotun Jos da aka shigar da kararsu, Mai Sharia Daniel Longji.

KU KARANTA: Jama’a da dama sun bata yayin da mayakan Boko Haram sun kai samame cikin dare

Sai dai dukkanin mutanen su 19 sun musanta tuhume tuhume guda biyu da ake musu daya danganci sa hannu ko wata masaniya game da kisan Alkali a zaman kotun na ranar Laraba 7 ga watan Nuwamna, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Fiye da lauyoyi 100 sun bayyana niyyarsu ta kare mutane 19 da suka kashe janar Alkali

Janar Alkali
Source: UGC

“Fiye da lauyoyi 120 na ta kokarin ganin sun kare wadanda ake tuhuma, sai dai har yanzu kotu bata bada belinsu ba, amma mun mika bukatar bada belinsu, kuma dukkaninsu sun musanta aikata laifin.” Inji Zi.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Filato, DSP Typove Mathias ya bayyana ma majiyarmu cewa an gurfanar da mutanen ne akan tuhume tuhume guda biyu; Hadin kai wajen aikata miyagun laifuka da kuma laifin kisan kai.

“Ana tuhumarsu akan laifuka biyu, hadin kai wajen aikata miyagun laifuka kamar yadda yake a sashi na 97 da kisan kai kamar yadda yake a sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka na yankin Arewacin Najeriya, dukkaninsu sun musanta tuhume tuhumen.

“Kuma Alkali ya dage sauraron karar zuwa 10 ga watan Disamba don sauraron bukatar bada belinsu, sa’annan ya yi umarnin a ajiyesu a gidan kurkuku na garin Jos.” Inji Kaakakin Tyopev.

A ranar 3 ga watan Satumba ne aka kashe janar Alkali a kauyen Dura Du yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jahar Bauchi daga Abuja, anyi ta nemansa ba’a ganshi na tsawon lokaci, daga bisani aka gano motarsa a cikin wani rafi dake garin, bayan wani lokaci kuma aka gano gawarsa a cikin rijiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel