‘Daliban Najeriya sun ba Gwamnati kwana 7 ta sasanta da Kungiyar ASUU

‘Daliban Najeriya sun ba Gwamnati kwana 7 ta sasanta da Kungiyar ASUU

Mun samu labari daga Jaridar nan ta Vanguard cewa Kungiyar ‘Daliban Najeriyan kasar nan sun hurowa Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shawo kan bukatun Kungiyar ASUU ko kuma ta ji ba dadi.

‘Daliban Najeriya sun ba Gwamnati kwana 7 ta sasanta da Kungiyar ASUU

Kungiyar NANS ta nemi Gwamnatin Tarayya ta shawo kan yajin ASUU
Source: UGC

Kungiyar NANS ta ‘Daliban Najeriya sun nemi Gwamnatin Tarayya ta cika duk yarjejeniyar da ta dauka da Kungiyar Malaman Jami’a watau ASUU. Kungiyar NANS ta ba Gwamnatin Najeriya wa’adin mako guda ne ta yi wannan aiki.

Shugabannin ‘Daliban na Najeriya a karkashin lemar NANS sun bayyana cewa za su soma zanga-zanga a fadin kasar nan idan har Gwamnati ba ta cika alkawuran da tayi wa Malaman Jami’a a Watan Oktoban bara cikin kwanaki 7 ba.

Sakataren yada labarai na Kungiyar ta NANS Mista Azeez Adeyemi ya bayyanawa manema labarai a Garin Abeokuta cewa ‘Daliban Najeriya za su fara yi wa Gwamnatin Tarayya zanga-zanga idan har ba ta yi wa ASUU yadda ta ke so ba.

KU KARANTA: Mu na cikin wani mawuyacin hali – Sojojin Najeriya sun fadawa Ministan Buhari

Adeyemi yace Gwamnatin Buhari ba ta cika alkawuran da tayi wa Malaman na Makarantun Jami’a a Oktoban 2017 ba. A dalilin haka ne ‘Daliban kasar su kace ba za su zuba ido su na kallon Gwamnati tana yin sakaci da harkar ilmi ba.

Azeez Adeyemi yace Gwamnatin Najeriya tayi wa harkar ilmi rikon sakainar kashi domin yaran manya su na karatu ne a Kasashen ketare don haka ba su damuwa don an bar harkar ilmi ya tabarbare a Najeriya na shekara da shekaru.

Yanzu dai ‘Daliban kasar ta reshen NANS sun ba Gwamnati rashin gaskiya a yajin aikin da Malaman Jami’o’i su ka tafi kwanan nan inda su ka kuma nemi a yi adalci wajen yakar barayin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel