Jama’a da dama sun bata yayin da mayakan Boko Haram sun kai samame cikin dare

Jama’a da dama sun bata yayin da mayakan Boko Haram sun kai samame cikin dare

Wasu mayakan Boko Haram sun kai mugun samame a yankin kudancin jahar Borno a daren Talata, inda suka yi sacen sacen kayayyakin abinci, daga bisani suka banka ma duk wani gida dake kauyen wuta, suka tsere, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito cewar a sakamakon wannan harin mazauna kauyen na Kala dake kusa da karamar hukumar Damboa sun yi batan dabo, ko sama ko kasa an nemesu an rasa har bayan tafiyan yan ta’addan.

KU KARANTA: Jerin wasu sabbin jami’ai da Buhari ya rantsar dasu manyan mukamai a hukamar NPC, da CCB

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewa da misalin karfe 9 na daren Talata yan ta’addan suka kunno kai cikin kauyen, inda suka bude ma mazauna kauyen wuta irin na mai kan uwa da wabi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu, wasu kuma suka jikkata.

Jama’a da dama sun bata yayin da mayakan Boko Haram sun kai samame cikin dare

Boko haram
Source: UGC

Majiyar yace bayan sun firgita jama’an kauyen, sai kuma suka shiga sace sacen kayan abinci, hatsi, har ma da dabbobi, nan da nan kuma suka banka ma kauyen wuta, daga nan ne suka afaka cikin dazukan daek zagaye da kauyen suka tsere.

“Muna cikin masifa kuma babu abinda zamu iya yi, kauyenmu bai wuce kilomita 2 daga garin Damboa ba, amma duk da haka mayakan Boko Haram suka kawo mana hari, suka sassace mana abincinmu, shanu, akuyoyi da kekuna.” Inji shi.

Sai dai wata majiya daga rundunar Sojojin Najeriya ya karyata labarin mazauna kauyen, inda yace Sojoji sun yi artabu da mayakan na Boko Haram da manyan bindigu, kuma daga karshe sun samu nasarar tarwatsasu har ma suka tsere daga kauyen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel