Gwamnonin da su ka bayyana a fili cewar za su iya biyan ma fi karanci albashi

Gwamnonin da su ka bayyana a fili cewar za su iya biyan ma fi karanci albashi

A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu ya karbi rahoton kwamitin da ya kafa domin yin bitar albashin ma'aikata da kuma fitar da sabbin alkaluman ma fi karancin albashin da ya dace a biya ma'aikacin gwamnati..

An dai kai ruwa rana tsakanin gwamnonin Najeriya, gwamnatin tarayya, da kuma kungiyar kwadago a kan batun karin albashin.

Kungiyar kwadago ta yi yajin aiki na jan kunne tare da bayyana cewar za ta tsunduma yajin aiki na sai baba-ta-gani a ranar 6 ga watan Nuwamba matukar gwamnati ba mayar da ma fi karancin albashi ya koma N30,000 ba.

Kafin zuwan ranar ne gwamnonin Najeriya su ka yi tayin cewar za su biya N24,000 a matsayin ma fi karancin albashi, tayin da kungiyar kwadago ta yi watsi da shi.

Gwamnonin da su ka bayyana a fili cewar za su iya biyan ma fi karanci albashi

Gwamnoni
Source: Depositphotos

Sai dai ko a lokacin da ake jayayya a kan adadin kudin da ya kamata ya kasance albashi ma fi karanci, wasu gwamnonin sun amsa cewar a shirye su ke su biya ko nawa ne, yayin da wasu kuma su ka ambaci adadin da za su iya biya.

DUBA WANNAN: Saraki ya yi canje-canje a wasu mukaman majalisa, duba

Daga rahotanni da kuma hira da aka yi da gwamnoni daban-daban, an samu gwamnoni 6 da su ka bayyana niyyar su ta biya ma fi karancin albashin, ko da kuwa ya zarce N30,000.

Gwamnonin su ne:

1. Badaru Abubakar na jihar Jigawa

2. Godwin Obaseki na jihar Edo

3. Nyesom Wike na jihar Ribas

4. Dakta Abdullahi Umar Ganduje

5. Victor Okezie Ikpeazu na jihar Abia

6. Willie Obiano na jihar Anambra.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel