Ku warware matsalar da ke tsakaninku da ASUU - Majalisar dattiaji ga gwamnatin tarayya

Ku warware matsalar da ke tsakaninku da ASUU - Majalisar dattiaji ga gwamnatin tarayya

- A ranar Laraba, majalisar dattijai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta warware matsalar da ke tsakaninta da kungiyar malaman jami'o'i na kasa (ASUU)

- Shehu Sani, sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ra tsakiya ya ce dukkanin dalilan da ASUU ta gabatar na gaskiya ne kuma bukatunsu na ci gaban ilimi ne gaba daya

- Dr. Bukola Saraki ya ce yana da kyau gwamnatin tarayya ta girmama yarjejeniyar da ta kulla tsakaninta da kungiyar ASUU tare da hanzarin kawo mafita ga wannan lamari

A ranar Laraba, majalisar dattijai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta warware matsalar da ke tsakaninta da kungiyar malaman jami'o'i na kasa (ASUU), don kawo karshen yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar ta shiga a jami'o'in da ke fadin kasar.

Sanata Barau Jibrin, daga mazabar Kano ta Arewa ne ya dago da zance kan yajin aikin a zaman da majalisar da gudanar, inda ya ke karanta wasu bangarorin bayanai na 42 da na 52.

A cewar majalisar dattijan, kamar yadda ta wallafa a shafintra na Twitter, ta ruwaito Shehu Sani, sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ra tsakiya yana cewa, "Nigeria ta dade tana warware sha'anin yajin aiki. Dukkanin dalilan da ASUU ta gabatar na gaskiya ne. Bukatunsu na ci gaban ilimi ne gaba daya. Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta warware wannan lamari da ke tsakaninta da ASUU."

KARANTA WANNAN: Jihar Delta: An tsinci gawar wani dan sanda yashe a cikin rami

Ku warware matsalar da ke tsakaninku da ASUU - Majalisar dattiaji ga gwamnatin tarayya

Ku warware matsalar da ke tsakaninku da ASUU - Majalisar dattiaji ga gwamnatin tarayya
Source: Depositphotos

Sanata Mao Ohuabunwa daga jihar Abia, ya ce: "Yana da muhimmaci ace gwamnati tana aiwatar da ayyukan da ya zamar mata wajibi ta yi su. Mune muka sanya baki a yajin aikin da ASUU ta shiga kwanan baya, kuma muka yi mata alkawarin cika mata bukatunta, amma gwamnati ta watsa mana kasa a ido."

Daga karshe dai, majalisar dattijai ta cimma matsaya na bukatar ma'aikatar ilimi da kwadago da ma dai sauran takwarorinsu da su zauna don warware matsalar da ke tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya don kawo karshen wannan yajin aiki da ASUU ta shiga.

"Yana da kyau gwamnatin tarayya ta girmama yarjejeniyar da ta kulla tsakaninta da kungiyar ASUU tare da hanzarin kawo mafita ga wannan lamari." a cewar shugaban majalisar dattijan, Dr. Bukola Saraki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel