Wani mutum ya datse kan shugaban matasa a karamar hukumar Oshiomhole

Wani mutum ya datse kan shugaban matasa a karamar hukumar Oshiomhole

Rundunar 'yan sanda a jihar Edo ta kama wani mutum mai suna Jimoh Odion bisa kisan wani shugaban matasa a karamar hukumar Etsako ta gabas.

Lamarin ya faru ne a wani kauye mai suna Jattu.

Odion ya kashe Atogwe Asilemhe, shugaban matasa, ta hanyar yi masa kwanton bauna tare da buge shi da fartanya kafin daga bisani ya saka adda ya datse ma sa kai.

Jaridar Punch ta rawaito cewar Odion ya cika wandonsa da iska tare da buya a wata coci bayan ya kisan Asilemhe.

Wani mutum ya datse kan shugaban matasa a karamar hukumar Oshiomhole

Wani mutum ya datse kan shugaban matasa a karamar hukumar Oshiomhole
Source: Depositphotos

Da yake bajakolin mai laifin ga manema labarai, kwamishinan 'yan sanda a jihar Benin, Johnson Kokumo, ya ce an kashe Asilemhe ne yayin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa wurin aiki tare da bayyana cewar Odion ya aikata laifin ne shi kadai.

DUBA WANNAN: 'Yan kasuwa sun yiwa El-Rufai ihu, sunyi watsi da tayin da ya yi musu

"A ranar 14 ga watan Oktoba ne wani mai suna Osilema da ke zaune a kauyen Ayogwiri ya kai rahoton kisan dan uwansa a ofishin hukumar 'yan sanda na kauyen Jattu da misalin karfe 12 na rana. Ya sanar da jami'anmu cewar wani mutum mai suna Jimoh Odion ne ya kashe dan uwan nasa, mai shekaru 46, ta hanyar girbe ma sa kai yayin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa wurin aiki."

A nasa bangaren, Odion, ya bayyana cewar ya kashe Asilemhe ne saboda ya yi masa gorin rashin ganinsa a wurin wani sha'anin jama'a.

A cewar sa, "Ni ne na kashe shi. Ban san me yasa na kashe shi ba don babu wata matsala a tsakaninmu.

"Ya yi min gorin rashin ganina a wani sha'anin jama'ar garinmu saboda akwai matsala tsakani na da maigari. Tun bayan lokacin ban san me yake faruwa da ni ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel