Jihar Delta: An tsinci gawar wani dan sanda yashe a cikin rami

Jihar Delta: An tsinci gawar wani dan sanda yashe a cikin rami

- An gano gawar wani jami'in rundunar 'yan sanda, Sifeta Samuel Onwueriegbo a yashe cikin wani babban rami, bayan watanni 3 da barinsa gida

- Har zuwa yanzu, babu wani tabbaci kan silar mutuwar tasa, da kuma yadda aka yi har gawar ta shiga cikin ramin

- Majiya daga rundunar 'yan sanda, ta ce an gano gawar dan sandan ba tare da wasu raunuka a jikinsa ba, kana aka garzaya da gawar zuwa dakin ajiyar gawarwarki don bincike

An gano gawar wani jami'in rundunar 'yan sanda, mai shekaru 51 da haihuwa, wanda aka bayyana sunansa da Sifeta Samuel Onwueriegbo a yashe cikin wani babban rami, kan hanyar Ekwuoma, kusa da Owerri-Olubor, karamar hukumar Ika ta Arewa-maso-Gabas.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, marigayin, wanda aka gano gawarsa a daren ranar Litinin, na aiki ne da rundunar 'yan sandan PMF ta 22, da ke Legas.

Har zuwa yanzu, babu wani tabbaci kan silar mutuwar tasa, da kuma yadda aka yi har gawar ta shiga cikin ramin, tun bayan da ya bar gidansa da ke Iyana-Iyesi, jihar Ogun, a ranar 13 ga watan Satumba, 2018.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Buhari ya bugi kirji kan samun nasara a zaben 2019 ko da WAEC ko babu

Jihar Delta: An tsinci gawar wani dan sanda yashe a cikin rami

Jihar Delta: An tsinci gawar wani dan sanda yashe a cikin rami
Source: Depositphotos

Wata majiya ta shaidawa The Nation cewar matar marigayin, Joy, ta shaidawa 'yan uwan mamacin tun a wancan lokaci cewar, mijin nata ya bar gida ba tare da sanar da ita inda zai je ba. A ranar 14 ga watan Satumba, da misalin karfe 1 na dare, 'yan uwan mamacin suka shigar da karar bacewarsa a ofishin rundunar 'yan sanda.

A ranar 20 ga watan Satumba, matar 'dan sanda ta shirya wani taro kan neman mijin nata, inda a nan ne kuma ta samu rahoton cewa anga mijin nata a jihar Delta. Binciken da ya gano gawar d'an sanda a cikin babban ramin.

Wata majiya daga rundunar 'yan sanda, ta bayyana cewa an gano gawar dan sandan ba tare da wasu raunuka a jikinsa ba. Daga nan ne kuma aka garzaya da gawar zuwa dakin ajiyar gawarwarki don ci gaba da bincike.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel