Kungiyar USIP ba tayi harsashen wanda zai lashe zabe a Najeriya ba

Kungiyar USIP ba tayi harsashen wanda zai lashe zabe a Najeriya ba

Kwanan nan aka yi ta yada labari a Jaridun gida cewa Kasar Amurka tace duk ta kare APC za tayi nasara a zaben da za ayi a Najeriya a 2019 inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zarce a kan kujerar sa.

Kungiyar USIP ba tayi harsashen wanda zai lashe zabe a Najeriya ba

Kasar Amurka ta karyata cewa tace Buhari zai ci zaben 2019
Source: Facebook

Kasar Amurka ta karyata cewa ta ba wani nasara a zaben da za ayi a Najeriya shekara mai zuwa. Kungiyar USIP da aka kafa a Amurka domin wanzar da zaman lafiya ta bayyana cewa sam ba ta tsoma bakin ta cikin siyasar Najeriya ba.

Kungiyar ta USIP tayi wannan karin haske ne a wani gajeren jawabi da ta fitar a makon nan inda ta musanya rahoton da Jaridar This Day ta fitar kwanaki. USIP tace babu ruwan ta da yin harsashe game da zabukan Najeriya ko wata kasa.

KU KARANTA: Atiku zai yi wa Buhari dukan babban bargo a zaben 2019 - Saraki

USIP tace ta fitar da wani rahoto game da zaben 2019 kwanaki amma babban abin da ke gaban ta shi ne ganin an yi zabe babu tashin hankali a kasar da sauran kasashen Duniya amma ba bayyana wanda zai yi nasara ko ya sha kashi a zabukan ba.

Kungiyar ta Amurka dai ta na ta kira ne da babban murya cewa ayi zabe ba tare da an yi rigima a Najeriya ba. Hakan ya sa Kungiyar ta hada kai da Malamai da ‘Yan siyasa, ‘Yan jarida. Da ‘Yan Boko da sauran jama’a don a zauna lafiya a 2019.

A jawabin da fitacciyar kungiyar tayi ta jadadda cewa babu abin da ya hada ta da nuna banbanci ko shiga cikin siyasa dumu-dumu illa iyaka neman ganin zaman lafiya ya samu a lokacin zabe a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel