Da duminsa: Tangardar na'urar magana ta sa an dage zaman majalisar wakilan tarayya

Da duminsa: Tangardar na'urar magana ta sa an dage zaman majalisar wakilan tarayya

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu yanzu daga jaridar Punch, na nuni da cewa majalisar wakilai ta tarayya, ta dage zaman da ta ke kan gudarwa a yau Laraba, sakamakon tangardar da na'u'rorin magana suka samu na cikin dakin taron majalisar.

Tun a ranar Talata ne dai zaman majalisar ke samun tangarda, wanda matsalar na'urar ke tilasta wasu mambobi barin kujerunsu zuwa wasu kujerun don samun damar yin magana.

A ranar Larabar nan, kakakin majalisar wakilan tarayyar, Rt. Hon. Yakubu Dogara, wanda ya harzuka da yadda na'urorin maganar ke bayar da matsaya, ba tare da zaton kowa ba, ya sanar da dage zaman majalisar har sai zuwa ranar Alhamis.

Cikakken rahoton yana zuwa...

KARANTA WANNAN: Rabon mukamai: Buhari ya roki majalisar dattijai ta amince da Izuwah a matsayin shugaban ICRC

Da duminsa: Tangardar na'urar magana ta sa an dage zaman majalisar wakilan tarayya

Da duminsa: Tangardar na'urar magana ta sa an dage zaman majalisar wakilan tarayya
Source: UGC

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta kasa da ta amince da Mr. Chidi Izuwah a matsayin sabon babban daraktan hukumar da ke kula da tace manya-manyan ayyuka na kasa (ICRC).

Shugaban kasa Buhari, a cikin wata wasika da ya aika mai kwanan wata 19 ga watan Oktoba, ya roki majalisar da ta yi kyakkyawan nazari tare da amincewa da wannan bukata tasa.

Shugaban majalisar dattijai, Dr. Bukola Saraki ne ya karanta wannan wasika a zaman da majalisar ta yi a jiya Talata, 6 ga watan Nuwamba, 2018.

Haka zalika, shugaban kasa Buhari ya mika kokon bararsa ga majalisar dattijan da ta amince da Mr Kabir Nakura a matsayin sabon shugaban hukumar kididdiga ta kasa, (NBS).

Bukatar hakan na kunshe a cikin wasikar da aka aikawa shugaban majalisar dattijan, Dr. Bukola Saraki, mai dauke da kwanan wata, 24 ga watan Oktoba, 2018.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel