Babu hanyoyi ko ina ka shiga a Kasar nan saboda irin mulkin PDP – inji Shugaban kasa Buhari

Babu hanyoyi ko ina ka shiga a Kasar nan saboda irin mulkin PDP – inji Shugaban kasa Buhari

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Kungiyar ARCAN ta tsofaffin Jakadun Najeriya a fadar Aso Villa kwanan inda ya koka da yadda aka mulki kasar nan a nan baya kadan.

Babu hanyoyi ko ina ka shiga a Kasar nan saboda irin mulkin PDP – inji Shugaban kasa Buhari

Babu lungu da sakon da ban ratsa ba lokacin ina neman zabe – Buhari
Source: Depositphotos

Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin Jagoran Kungiyar tsofaffin Jakadun Najeriya a kasashen Duniya wanda Ambasada Oladapo Fafowora ya jagoranta. Shugaban kasar ya bayyanawa tsofaffin Jakadun halin da Najeriya ta ke ciki.

Buhari yake cewa ya zagaye kaf Najeriya a lokacin yana yawon neman mulki inda ya ganewa kan sa yadda hanyoyi su ka lalace a Kasar nan. Haka kuma Shugaban kasar yace maganar wutan lantarki ya tabarbare a lokacin mulkin PDP.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa za su bankado badakalar tallafin man fetur a Gwamnatin Buhari

Har ila yau, Shugaba Buhari yace Najeriya ta yi rashi kwarai da gaske daga 1999 zuwa 2015 a Gwamnatin PDP domin kuwa babu abin da aka yi wa Kasar. Buhari ya kuma koka da yadda aka sace Dala Biliyan 16 da sunan gyara wutan lantarki.

Tsofaffin Jakadun na Najeriya sun nemi Gwamnatin Buhari ta duba batun kudin fanshon su da kuma ginin Hedikwatar su da aka gaza karasawa. Fafowora ya kuma nemi a rika sakin kudi yadda ya kamata a Ma’aikatar harkokin kasar waje.

A jawabin Shugaban kasar yace yanzu abubuwa sun fara mikewa a kasar dalilin yarjejeniyar da ka shiga da China na gina layin dogo. Shugaban kasar ya kuma nemi Ma’aikata su rika la’akari da kokarin da yake yi duk da karancin kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel