Yanzu Yanzu: An samu hargitsi a majalisa kan manufofin gwamnatin Buhari

Yanzu Yanzu: An samu hargitsi a majalisa kan manufofin gwamnatin Buhari

- Zauren majalisar dattawa a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba ta rincabe da hayaniya

- Hakan ya biyo bayan zargin da shugaban marasa rinjaye ta yi akan manufofin Gwamnatin Buhari

- Olujimi ta yi zargin cewa an bukaci wadanda suka amfana daga shirin da su bayar da cikakken bayanin katin zaben su a cikin fam din shirin

Zauren majalisar dattawa a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba ta rincabe da hayaniya lokacin da shugaban marasa rinjaye a majalisar, Sanata Biodun Olujimi ta yi korafi akan shirin kyautata wa jama’a na Gwamnatin Tarayya, wanda gwamnatin Buhari ta samar.

A cewar Olujimi ta yi zargin cewa an bukaci wadanda suka amfana daga shirin da su bayar da cikakken bayanin katin zaben su a cikin fam din shirin.

Yanzu Yanzu: An samu hargitsi a majalisa kan manufofin gwamnatin Buhari

Yanzu Yanzu: An samu hargitsi a majalisa kan manufofin gwamnatin Buhari
Source: Depositphotos

Yayinda ta gabatar da kwafin fam din, ta kuma yi zargin cewa an rubuta Ïna tare da Buhari” a jikin fam din.

KU KARANTA KUMA: Babu hanyoyi ko ina ka shiga a Kasar nan saboda irin mulkin PDP – inji Shugaban kasa Buhari

Kafin shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Ahmad Lawan wanda ke kare gwamnatin Buhari ya yi Magana kan shirin, har majalisar ta kaure da hayaniya inda mambobin APC da PDP k eta musayar kalau.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa kuma darakta janar na kungiyar kamfen din dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa dan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar zai lashe kuri’u a zaben 2019.

Saraki ya bayyana cewa duba ga goyon bayan yan Najeriya da dan takarar shugaban kasa na PDP ke samu babu shakka za su yi nasara a zaben Fabrairun 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel