Ba bu wani shiri na kara albashin yan majalisa – Saraki ga SERAP

Ba bu wani shiri na kara albashin yan majalisa – Saraki ga SERAP

- Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya karyata shirin kara albashin yan Najeriya a Najeriya

- Saraki ya gargadi SERAP da ta san irin bayanin da za ta dunga yadawa jama’a, musamman kasancewarta kungiya da ake mutuntawa

- SERAP ta aika wani sako ga shugaban majalisar dattawa cewa zargin shirin kara albashin yan majalisa ya saba ma dokar kasar

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba ya mayar da martani ga SERAP kan zargin cewa ana shirin yiwa yan majalisar dokokin kasar karin albashi.

Saraki ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan kafofin watsa labarai, Olu Onemola ya bayyana hakan yayinda yake martani ga zargin SERAP na cewa yan majalisa na shirin kara albashin su.

“Ya SERAP, ba bu makamancin wannan zargi na Karin alawus din sanatoci.

“Akwai bukatar kungiya kamar ta ku su dunga taka-tsan-tsan, musamman wajen aika bayanai ga al’umma. Mun gode,” cewar Onemola a sahfin twitter.

Ba bu wani shiri na kara albashin yan majalisa – Saraki ga SERAP

Ba bu wani shiri na kara albashin yan majalisa – Saraki ga SERAP
Source: Depositphotos

SERAP ta aika wani sako ga shugaban majalisar dattawa cewa zargin shirin kara albashin yan majalisa ya saba ma dokar kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake hana El-Zakzaky beli

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa kuma darakta janar na kungiyar kamfen din dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa dan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar zai lashe kuri’u a zaben 2019.

Saraki ya bayyana cewa duba ga goyon bayan yan Najeriya da dan takarar shugaban kasa na PDP ke samu babu shakka za su yi nasara a zaben Fabrairun 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel