Yajin aikin kungiyar ASUU: Mun bi umurnin uwar kungiya sau da kafa - UNILAG

Yajin aikin kungiyar ASUU: Mun bi umurnin uwar kungiya sau da kafa - UNILAG

- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU reshen jami'ar Legas (UNILAG), ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani kamar yadda kwamitin zartaswar kungiyar na kasa ya umurta

- Shugaban kungiyar na jami'ar, Dr Dele Ashiru, ya ce mambobin kungiyar na jami'ar sun gudanar da taro a ranar Talata, inda suka yanke bin umurnin uwar kungiyar na shiga yajin aikin

- ASUU ta shiga wannan yajin aikin ne a fafutukar da take yi na ganin cewa gwamnati ta cika akawarin da ta daukar mata a shekarar 2009

Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU reshen jami'ar Legas (UNILAG), ta ce ta bi umurnin uwar kungiya sau da kafa na shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani kamar yadda kwamitin zartaswar kungiyar na kasa ya umurta.

Shugaban kungiyar na jami'ar, Dr Dele Ashiru, ya bayyana hakan a wata zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Laraba a Legas, inda ya ce mambobin kungiyar na jami'ar sun gudanar da taro a ranar Talata, inda a nan ne suka yanke shawarar marawa uwar kungiyar baya wajen shiga yajin aikin.

NAN ta ruwaito cewa a ranar Lahadi ne kungiyar malaman jami'o'in ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani a fadin kasar, bayan da ta gudanar da wani taron shuwagabanni da masu ruwa da tsaki a jami'ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Akure.

KARANTA WANNAN: Sabon tarihi: Ilhan Omar, Rashida Tlaib sun zama Musulmai na farko a majalisar wakilan Amurka

Yajin aikin kungiyar ASUU: Mun bi umurnin uwar kungiya sau da kafa - UNILAG

Yajin aikin kungiyar ASUU: Mun bi umurnin uwar kungiya sau da kafa - UNILAG
Source: UGC

Kungiyar dai ta shiga wannan yajin aikin ne a fafutukar da take yi na ganin cewa an samar da karin kudaden daukar nauyin ayyukan jami'o'in gwamnatin tarayya, da kuma gazawar gwamnati na cika akawarin da ta daukar masu a shekarar 2009.

Haka zalika, kungiyar na adawa da wani yunkuri da take zargin gwamnatin tarayya na yi na karawa dalibai kudin makaranta da kuma samar da bankunan makarantu.

A cewar Ashiru, yajin aikin ya shafi gaba daya ayyukan jami'ar ta Legas. Dangane da rokon da gwamnatin tarayya ta yi na ASUU ta hakura da wannan yajin aikin, Ashiru ya ce bakin alkami ya riga da ya bushe, don rokon ya zo a makararren lokaci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel