Rikicin APC: Oshiomole ya raba kan gwamnonin APC 6

Rikicin APC: Oshiomole ya raba kan gwamnonin APC 6

Kan gwamnonin yankin Yarbawa shida ya rabu kan shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Adams Oshimohole, Legit Hausa ta samu rahoto.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa yayinda wasu na kokarin ganin cewa an cire Oshiomole daga kujerarsa bisa ga rikicin da ya kawo jam’iyyar, wasu sun ce babu yadda za’ayi a ciresa.

Wadanda suka yi mubaya’a ga Oshiomole sune gwamnonin da ke biyayya ga babban jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kunshi gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode; gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola; gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Gwamnonin suke yiwa Oshiomole tawaye sune gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun da gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu. Sun kulla gaba da Oshiomole ne sanadiyar abinda ya musu a zaben fidda gwanin jam’iyyar a jihohinsu.

KU KARANTA: Hukumar yan sanda ta damke hafsoshinta 4 dake da hannu cikin harin gidan Ekweremadu

Wadannan gwamnoni biyu sun sake ganawa da shugaba Muhammadu Buhari ranan Lahadi. Daga baya, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya hadu da su wanda ke nuna cewa yana tare da su wajen adawa da Oshiomole.

Amma wata majiya mai karfi na bayyana cewa tsohon ministn bai da matsala da shugabancin Adams Oshiomole.

Zmu tun mun kawo muku cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da kokarin kashe wutar da ta kunno kai a tsakar gidar jam’iyyar APC sakamakon takun saka da ta shiga tsakanin shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole da wasu gwamnoni hudu, da a yanzu suke barazanar sauya sheka.

Majiyar Legit.com ta ruwaito daga cikin wadannan gwamnoni akwai Anayo Rochas Okorocha na jahar Imo, Ibikunle Amosun na jahar Ogun, Rotimi Akeredeoulu na jahar Ondo da kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdul Azeez Yari na jahar Zamfara.

Wannan sabuwar takaddama tsakanin Oshiomole da jiga jigan gwamnonin, har ma da wasu manyan yayan jam’iyyar, musamman Sanatoci ta faru ne a sanadiyyar zaben fidda gwani nay an takarkaru daya gudana a kwanakin baya, wanda ya bar baya da kura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel