Hukumar yan sanda ta damke hafsoshinta 4 dake da hannu cikin harin gidan Ekweremadu

Hukumar yan sanda ta damke hafsoshinta 4 dake da hannu cikin harin gidan Ekweremadu

- Hukumar yan sanda tana binciken hafsoshinta hudu kan harin gidan Ekeremadu

- Hukumar ta bayyana cewa daya daga cikin maharani mai suna, Mohammed Yusuf, na hannu yayinda abokin aikinsa Ali y arce

-Hukumar ta karyata maganar cewa ta yi jinkiri wajen kawowa Sanatan agaji

Hukumar yan sanda Najeriya ta sanar da cewa ta damke hafsoshinta hudu kan harin da aka kaiwa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, a gidansa dake Apo ranan Talata, 6 ga watan Nuwamba, 2018.

A wasikar da hukumar ta turowa Legit.ng, ta musanta cewa ta yi jinkiri wajen amsa kiran Ekweremadu yayinda aka far masa.

KU KARANTA: Mambobin APC 20,000 a garin Akpabio sun sheka PDP, rikici ya barke a garin

Kakakin hukumar, DCP Jimoh Moshood yace:

“Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike kan wani laifi kuma daya daga cikin masu laifin, Mohammed Yusuf, dan garin Kaura Namoda ya amince da bayyana gaskiyan al’amarin. Kana ya ambaci sunan wani Ali wanda ya arce.” “

“Daga cikin abubuwan da aka kama hannunsu shine na’urar daga mota, sukun direba, rodu, wuka, da wasu kayayyakin balla gida.”

Mun kawo muku rahoton cewa Majalisar dattawan Najeriya ta umurci kwamitin harkokin hukumar yan sanda da ta kaddamar da bincike kan harin kisan da aka kaiwa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, da iyalansa a birnin tarayya Abuja.

Ekweremadu ya laburta yadda wannan abu ya faru a filin majalisa a yau. Ya kara da cewa an samu nasarar damke daya daga cikin yan bindigan.

Sanata Ekweremadu ya nuna rashin jin dadinsa ga rashin zaburar jami’o’in tsaron Najeriya, ya bayyana cewa ya kira sifeton yan sanda da kansa amma a kashe take.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel