Fusatattun matasa sun kashe matasa 2 kan satar wayar iphone da kwamfuta

Fusatattun matasa sun kashe matasa 2 kan satar wayar iphone da kwamfuta

- Wasu fusatattun matasa sun kashe wasu matasa biyu kan zargin sace wayar iphone da kuma na’urar kwamfuta a Benin

- Rundunar yan sandan jihar ba ta yi martani kan lamarin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoto

- Idon shaidan sun yi korafi kan rashin hakurin matasan da suka dauki doka a hannu ta hanyar kashe wadanda ake zargin su biyu

Rahotanni sun kawo cewa wasu fusatattun matasa sun kashe wasu matasa biyu kan zargin sace wayar iphone da kuma na’urar kwamfuta a Benin, babbar birnin jihar Edo.

Wasu mutane da ba su tabbatar da zargin bane suka far ma matasan wanda ba’a bayyana sunansu ba tukuna.

Koda dai rundunar yan sandan jihar ba su yi martani kan lamarin ba tukuna, wasu idanun shaida sun nuna rashhin jin dadi kan lamarin.

Idon shaidan sun yi korafi kan rashin hakurin matasan da suka dauki doka a hannu ta hanyar kashe wadanda ake zargin su biyu.

Fusatattun matasa sun kashe was yara 2 kan satar wayar iphone da kwamfuta

Fusatattun matasa sun kashe was yara 2 kan satar wayar iphone da kwamfuta
Source: Depositphotos

Wani idon shaida da ya nemi a boye sunansa, ya ce: “Fusatattun matasa sun kashe yaran biyu a garin Benin saboda su zarge su da satar wata wayar iphone da kwamfutar tafi da gidanka, abun bakin ciki ne da kaico.

“Wannan mutane da suka dauki doka a hannu sune kuma za su je shafin twitter suna kalubalantar sojoji da harbin masu zanga-zanga wanda suka jefe su da duwatsu.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake hana El-Zakzaky beli

Yan sanda za su rigada sun yi maratani kan lamarin ba a lokacin wannan raoto.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel