Kotu ta soke sabbin nade-naden sarauta da El-Rufai ya yi a Kaduna

Kotu ta soke sabbin nade-naden sarauta da El-Rufai ya yi a Kaduna

A safiyar yau ne babban kotu na II da ke zamanta Zaria da soke nadin wasu sabbin masu unguwani da gwamna Nasir El-Rufai ya yi a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kotun ta umurci dukkan masu unguwanin da gwamnan ya tsige daga mukammansu su koma kan kujerunsu.

Kotu ta soke sabbin nade-naden saruatar da El-Rufai ya yi a Kaduna

Kotu ta soke sabbin nade-naden saruatar da El-Rufai ya yi a Kaduna
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: An takaita zirga-zirga a wasu sassan Kaduna saboda shari'ar El-Zakyzaky

A dai cikin kwana-kwanan nan ne gwamna El-Rufai Malam Nasir El-Rufai ya amince da yiwa Mai Martaba Dr. Danjuma Barde (Esu Chikun) wanda a baya akafi sani da Sa Gbagyi karin girma zuwa sarki mai daraja ta daya.

An fara yiwa Sa Gbagyi nadin sarauta ne a ranar 29 ga watan Disamban 2000 sannan ya kara aiki a ranar 18 ga watan Janairun 2001 a matsayin sarki mai daraja ta uku.

An yi masa karin girma zuwa sarki mai daraja na biyu a shekarar 2007. Sanarwan karin girmar da gwamnan ya yi masa yana dauke ne cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Samuel Aruwan a yau ranar Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel