Yadda zabuka suka gudana a jya a Amurka, ko Trump da jam'iyyarsa sun kai labari?

Yadda zabuka suka gudana a jya a Amurka, ko Trump da jam'iyyarsa sun kai labari?

- Anyi zaben majalisun Amurka na tsakiyar zango

- Jam'iyyar su Obama ta kwaci ta wakilai, tasu Bush ta ci gaba da rike ta Dattijai

- Shugaba Trump yace yaji dadin zaben

Yadda zabuka suka gudana a jya a Amurka, ko Trump da jam'iyyarsa sun kai labari?

Yadda zabuka suka gudana a jya a Amurka, ko Trump da jam'iyyarsa sun kai labari?
Source: UGC

Zaben kafa tarihi, wanda ya raba kan 'yan Amurka ya zo ya wuce, ya bar baya da qura, inda aka ga Jam'iyyarsu Obama ta dawo ta dauki majalisar wakilai, inda ita kuma ta su Trump ta ci gaba da rike majalisar Dattijai, kamar yadda aka yi a hasashe.

A yanzu kam, an sami matasa da yawa da suka fito don kunyata shugaba Trump, amma basu yi nasara a wasu jihohin ba, tunda suma na Republican sun fito don kare muradunsu, musamman a kujerun gwamna.

DUBA WANNAN: 'Yan shia na kokarin zare ma soji ido da lasar takobi

Su Obama dai na kokarin ganin sun jima shugaba Trump ne, ko don saboda su rage masa karfi kafin zuwa zabukan 2020, inda ake sa rai zai nemi tazarce.

Yanzu dai, an sami karin bakake da musulmi wadanda bangaren wasu turawan zafin kai basu so su yi mulki, sun ci zabe.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel