Cikin sirri: Shugaba Buhari ya ba surukin sa wani babban mukami a gwamnati

Cikin sirri: Shugaba Buhari ya ba surukin sa wani babban mukami a gwamnati

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari an sake bankado wata rashin kyautawar sa a mulki inda aka gano cikin sirri, yadda ya nada surukin sa a matsayin shugaban hukumar gwamnatin tarayya dake kula da cigaban al'ummomin yankunan kan iyakokin Najeriya watau Nigeria’s Border Communities Development Agency.

Wanda shugaban kasar ya ba shugabancin hukumar kamar yadda muka samu shine Junaid Abdullahi, tshohon matukin jirgin sama kuma mijin babbar diyar shugaban kasar Marigayiya Zulaihat wadda ta rasu a shekarar 2012.

Cikin sirri: Shugaba Buhari ya ba surukin sa wani babban mukami a gwamnati

Cikin sirri: Shugaba Buhari ya ba surukin sa wani babban mukami a gwamnati
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Kotun tarayya ta bayar da umurnin a kamo Oshiomhole

Legit.ng Hausa ta samu cewa Alhaji Junaid Abdullahi ya soma aiki a matsayin shugaban hukumar ne tun a ranar 18 ga watan Oktoban da ya gabata inda ya karbi shugabancin daga hannun Jummai Idakwo.

A wani labarin kuma, Akalla jami'iyan sojin Najeriya 149 ne yanzu haka ke fuskantar hukunci bisa samun su da laifin da hukumar rundunar su ta sojoji ta yi na anfani da soshiyal midiya ba bisa ka'ida ba a karo na farko tun bayan kafa masu sharuda da dokokin yin hakan.

Majiyar mu ta Premium Times ta samu cewa jami'an rundunar da aka samu da laifin dai yawancin su duk kananan sojoji ne kuma sun fito daga bangaren sojin kasa, na sama da ma na ruwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel