Fayose ya fallasa wani mugun kudurin gwamnatin Buhari a watan Mayu mai zuwa

Fayose ya fallasa wani mugun kudurin gwamnatin Buhari a watan Mayu mai zuwa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose ya gargadi gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da ta jingine kudurin ta na kara kudin man fetur daga Naira 145 a kan kowace lita zuwa N185 a watan Mayu na shekarar 2019 mai zuwa.

Fayose ya bayyana wannan kuduri a matsayin mummunan abu da ke shirin samun 'yan Najeriya daga gwamnatin musamman ma duba da maganar karin albashin da ma'aikatan kasar ke nema.

Fayose ya fallasa wani mugun kudurin gwamnatin Buhari a watan Mayu mai zuwa

Fayose ya fallasa wani mugun kudurin gwamnatin Buhari a watan Mayu mai zuwa
Source: Twitter

KU KARANTA: An yi musayar yawu tsakanin gwamnatin tarayya da hukumar WAEC

Legit.ng Hausa ta samu cewa Gwamnan ya kara da cewa karin kudin man da gwamnatin ke shirin yi tamkar wata hanya ce ta sake kwace 'yan kudin da gwamnatin zata karawa ma'aikata a wajen farashin na mai.

Haka zalika Fayose wanda ke zaman daya daga cikin manyan 'yan adawar shugaban kasar ya ce gwamnatin ta Buhari na ta kara jan kafa wajen dabbaka mugunyar manufar ta su har sai bayan zaben 2019 saboda keta.

A baya dai anyi ta rade raden cewa gwamnatin zata kara kudin mai jita-jitar da gwamnatin ta musanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel