Rikicin Shi’a: Jakadan Ingila ya koka da yadda ake kashe mutane a Najeriya
Mun samu labari daga Jaridu cewa Gwamnatin Kasar Birtaniya tayi Allah-wadai da rikicin da ya kaure tsakanin kungiyar IMN na Mabiya addinin Shi’a da kuma Jami’an tsaro na Gwamnatin Najeriya kwanaki.

Asali: Facebook
Kasar Birtaniya ta bakin wani Jakadan Kasar a Najeriya ta fitar da jawabi ta na mai kokawa kan mutanen da aka kashe a takaddamar da aka samu tsakanin ‘Yan Shi’a da Hukuma kwanan nan a cikin babban Birnin Tarayya Abuja.
Jakadan Kasar Birtaniya da ke nan Najeriya ya bayyana cewa ba su ji dadin yadda mutane fiye da 50 su ka rasa rayukan su wajen rigima da Jami’an tsaro ba. Kasar ta Birtaniya tace tana lura da duk abubuwan da ke wakana a cikin Najeriya.
KU KARANTA: Da wahala a iya tika Buhari da kasa a zaben 2019 - Kasar Amurka
A jawabin, Jakadan Kasar wajen ya nuna cewa su na da masaniyar mutanen da ke mutuwa a hannun Gwamnatin Najeriya inda ta kara jaddada cewa aikin Jami’an tsaro ne su kare rayukan jama’a kamar yadda dokoki su ka tanada.
Haka kuma Kasar ta nemi a gudanar da tsattsauran bincike game da abin da ya faru tare da daukar mataki na hukunta wadanda duk aka samu da laifi. Jakadan na Ingila yace dokar Kasa ta ba mutane damar yin zanga-zanga a ko ina.
‘Yan Shi’a dai su na ta faman zanga-zanga ne saboda tsare Jagoran Kungiyar IMN Sheik Ibrahim El-Zakzaky da Gwamnatin Najeriya ta ke cigaba da yi duk da cewa Kotu ta nemi a sake sa tun ba yau ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng