Dalilin yawan aukuwar rikita-rikita a jihar Kaduna

Dalilin yawan aukuwar rikita-rikita a jihar Kaduna

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, masu da ruwa da tsaki a jihar Kaduna sun danganta yawaitar aukuwar rikita-rikita a jihar a sakamakon gazawar gwamnati, rashin adalci da kuma tsananin kiyayya a tsakanin al'umma.

Kimanin rayukan mutane 70 ne suka salwanta a sakamakon rikita-rikitar da ta auku cikin fadin jihar a kwana-kwanan, yayin da aukuwar wannan mummunan lamari a halin yanzu ya zamto tamkar ruwan dare cikin shekaru 39 da suka gabata.

Masu da ruwa da tsaki na jihar yayin ganawa da manema labarai sun bayyana ra'ayoyinsu dangane da wannan mummunan lamari, inda mafi akasarin su suka alakanta wannan annoba da gazawar gwamnatin wajen hukunta ma su wannan laifi da rashin daukar kwararan matamakai.

Rikita-rikita da ke faman aukuwa tsawon shekaru 40 da suka gabata na da nasaba da yaduwar jita-jita, rashin aikin yi, da kuma tsanani adawa ta siyasa gami da kiyayyar juna da ta yi katutu cikin zukatan al'ummar jihar.

Gwamna Nasir El-Rufa'i tare da Shugaba Buhari yayin ziyararsa zuwa jihar Kaduna
Gwamna Nasir El-Rufa'i tare da Shugaba Buhari yayin ziyararsa zuwa jihar Kaduna
Asali: Facebook

Sheikh Jamilu Albani, babban mai bayar da shawara ta musamman lan harkokin addini ga gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai' ya bayyana cewa, babban musababbin ci gaba da aukuwar tashin-tashina a jihar tsawon shekaru 39 da suka gabata na da nasaba da gazawar gwamnati wajen daukar matakai da kuma rashin hukunta ma su hannu cikin wannan muguwar aika-aika.

Ya ke cewa, a sanadiyar rikon sakainar kashi daga bangaren gwamnati ya sanya ma su aikata wannan mummunan lamari ke ci gaba da cin Karen su ba bu babbaka a sanadiyar rashin daukar izina ta hukuncin doka ta aka rasa a jihar.

KARANTA KUMA: Tsinkewar Cutar Kwalara ta kwantar da Mutane 16, Rayukan 5 sun salwanta a jihar Gombe

Kazalika wani babban Malami na Addinin Kirista, Rabaran Isaac Gbadero da ke unguwar Sabon Gari a garin Zaria, ya danganta aukuwar tashin-tashina a jihar Kaduna da rashin adalci da addinai musamman daga bangaren 'yan siyasa da kuma rashin gaskiya ta Malaman Addinai.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar ta Kaduna domin ganawa da Sarakunan gargajiya, manyan Malaman Addinai da sauran masu ruwa da tsaki a yayin yunkuri na magance aukuwar wannan annoba a jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng