Karshen zance: Amurka ta shirya baiwa Atiku izinin shiga kasar ta

Karshen zance: Amurka ta shirya baiwa Atiku izinin shiga kasar ta

Dan takarar kujerar shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar a inuwar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya samu 'yar manuniya daga mahukunta a kasar Amurka dake nuna cewa za su iya bashi izinin shiga kasar su idan ya nema a wannan karon.

Gbenga Daniel dake zaman jagoran kungiyar Kamfe din Atiku watau Atiku Presidential Campaign Orgsanisation (APCO) shine ya bayyana hakan a cikin wata fira da yayi da wakilin gidan talabijin din Channels.

Karshen zance: Amurka ta shirya baiwa Atiku izinin shiga kasar ta

Karshen zance: Amurka ta shirya baiwa Atiku izinin shiga kasar ta
Source: Facebook

KU KARANTA: Tsohon mataimakin Gwamna Ganduje ya raba gari da Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta samu cewa shi dai Atiku Abubakar yana fuskantar matsin lamba ne daga 'yan Najeriya sakamakon rashin shigar sa kasar Amurka bisa wasu zarge-zargen da kasar ke yi masa na tafka almundahana dake da alaka da cin hanci da rashawa a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

Sai dai Gbenga Daniel din ya kara da cewa yadda ake ruruta lamarin siyasa ce kawai kuma tuni 'yan Najeriya sun soma gane hakan kuma su na da tabbacin cewa a zabe mai zuwa za su samu nasara don kuwa bai kamata zuwa Amurka kadai ya zama wani tarnaki ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel