Bango ya tsage: Jigo a PDP a jihar Jigawa ya fita daga jam'iyyar, ya shiga APC
- Tsohon kwamishinan shari'a gwamnatin PDP a jihar Jigawa, Mista Yakubu Ruba, ya canja sheka daga PDP zuwa APC
- Ruba ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira yau, Laraba, a Dutse, babban birnin jihar Jigawa
- Mista Yakubu Ruba, ya canja sheka daga PDP zuwa APC tare da magoya bayansa kusan mutum 10,000
Tsohon kwamishinan shari'a gwamnatin PDP a jihar Jigawa, Mista Yakubu Ruba, ya canja sheka daga PDP zuwa APC tare da magoya bayansa kusan mutum 10,000.
Ruba ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira yau, Laraba, a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
"Abinda kowa ya sani ne cewar na kasance dan jam'iyyar PDP tun daga farkon kafuwar ta har zuwa lokacin da ta fadi zabe a shekarar 2015.
"Na yi ma ta hidima da lokacina da rayuwa ta domin ta samu cigaba da kuma kare mambobinta.

Asali: Twitter
"Na tabbata duniya za ta bayar da shaidar irin hidimtawa da na yiwa PDP da ma 'yan jam'iyyar.
"Amma, saboda wasu dalilai da kuma yadda wasua cikin jam'iyyar PDP ke yiwa magoya baya na, na fuskanci cewar ba zan iya cimma burina na siyasa a jam'iyyar PDP ba.
DUBA WANNAN: Alkawarin da Buhari ya yiwa 'yan takarar APC da su ka fadi a zaben cikin gida
"Saboda wadannan dalilai ne na zabi ficewa daga jam'iyyar PDP daga yau.
"Duk da na fita daga PDP, ina mai mika godiya ga wasu daga mambobinta da su ka bani dama na yiwa jiha ta aiki a matsayin kwamishinan shari'a daga shekarar 2011 zuwa 2015.
"Da wannan nake sanar da dukkan magoya baya na da su fita daga PDP.
"A iya yau kadai, ni da magoya bayana fiye da 10,000 ne mu ka canja sheka daga PDP zuwa APC," in ji Ruba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng