Saboda tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta sawo makamai masu tarin yawa (Hotuna)
Rundunar sojin Najeriya sun sanar da karbar manyan makamai masu tarin yawa da suka siyo a lokutan baya wadanda za su yi anfani da su wajen tabbatuwar samuwar tsaro a cikin kasa.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wani rubutu da rundunar ta wallafa a shafin ta na dandalin sadarwar zamani tare kuma da hotunan makaman da ta siyo.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Legit.ng Hausa haka zalika dai ta samu cewa a cikin sanawar da rundunar sojin ta wallafa bata fadi daga inda makaman suka taho ba.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Idan dai mai karatu bai manta ba rundunar sojin ta Najeriya yanzu haka ta rarraba dakarunta a jahohi daban daban inda suke aikin tabbatar da zaman tafiya da kuma kwantar da tarzoma.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar Abuja, babban birnin tarayya sun sanar da samun nasarar cafke akalla 'yan shi'a almajiran Malam Zakzaky sakamakon artabu da dauki-ba-dadin da suke ta yi da su a ranar Talata.
Kwamishin 'yan sandan Bala Ciroma shine ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda suka kama din ga manema labarai a hedikwatar su dake a garin Abuja.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng