Karin bayani: Yadda ganawar Buhari da gwamnonin Kudu maso Kudu ta kasance
Rahoton da Legit.ng ke samu daga fadar shugaban kasa, na nuni da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawar sirri da gwamnonin Kudu maso Kudu guda hudu, a cikin fadar shugaban kasar, da ke Abuja.
Gwamnonin da shugaban kasa Buhari ya shiga wannan ganawar sirrin da su, sun hada da Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers; Seriake Dickson na jihar Bayelsa; Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom da kuma Ifeanyi Okowa na jihar Delta.
KARANTA WANNAN: Babbar magana: Wani lauya ya mari DPO tare da yaga masa kaki, ya kuma fasa kan DCO

Asali: Facebook
Kafamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, ganawar sirrin, na iya samun tattaunawa kan hukuncin kotun koli a ranar 24 ga watan Oktoba, dangane da jihohin da suka mallaki mai a yankunan Niger Delta.
Idan ba a manta ba, jihohin Rivers, Bayelsa, da Akwa Ibom sun kai kokensu ga kotun koli kan ta yi hukunci na kara masu kudaden shiga bisa la'akari da sashe 16 sakin layi na 1 a dokar kwangila da ke kunshe a kara mai lamba SC964/2016 da lauya Lucius Nwosu ya shigar a madadinsu.
Sashen dokar ya baiwa gwamnatin tarayya umurnin karin hannun jari kan kudaden shiga ga jihohi ma damar farashin danyen mai ua haura dala 20 akan kowacce ganga.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng